Kokarin Al'ummar Kasar Yemen Na Kawo Karshen Mamayar Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i24243-kokarin_al'ummar_kasar_yemen_na_kawo_karshen_mamayar_saudiya
Shugaban Majalisar kolin zartarwa ta kasar yemen yayi gargadin cewa duk wani harin da za a ci gaba da kaiwa kasar, Al'ummar yemen za ta ci gaba da kokarinta wajen 'yantar kasar daga mamaya.
(last modified 2018-08-22T07:00:43+00:00 )
Sep 21, 2017 15:31 UTC
  • Kokarin Al'ummar Kasar Yemen Na Kawo Karshen Mamayar Saudiya

Shugaban Majalisar kolin zartarwa ta kasar yemen yayi gargadin cewa duk wani harin da za a ci gaba da kaiwa kasar, Al'ummar yemen za ta ci gaba da kokarinta wajen 'yantar kasar daga mamaya.

Hukumar gidan radio da telbijin na kasar Iran ya nakalto Salih Samad Shugaban majalisar kolin zartarwa kasar yemen a wannan Alkhamis yayin da yake jawabi a gaban duban al'ummar kasar na zagayowar ranar 21ga satumba, shekaru uku kenan da kawancen saudiya ya fara kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar yana mai cewa duk harin da kawancen saudiya ke kaiwa cikin kasar babu wani da janyo face karin hadin kai na al'ummar kasar yemen wajen tunkarar mahukuntar masarautar saudiya.

Yayin da yake ishara kan neman kungiyoyin kasa da kasa da suyi kokari wajen kawo karshen hare-haren wuce gona da irin kan al'ummar kasar, Assamad ya ce shekaru uku kenan da al'ummar kasar suke fuskantar hare-haren zalinci  daga kawancen masarautar saudiya kuma babu wani abin rayuwa na al'ummar Yemen da wannan kawance bai kaiwa hari ba, domin haka ya zama wajibi ga kungiyoyin kasa da kasa su yi aiki da  nauyin da ya rataya kansu domin kawo karshen wannan yaki da kuma kiyaye al'umma da kasar Yemen.