Iraki/Kurdistan : Barzani Ya Kira Kurdawa Su Fito Jefa Kuri'a
(last modified Sun, 24 Sep 2017 15:56:53 GMT )
Sep 24, 2017 15:56 UTC
  • Iraki/Kurdistan : Barzani Ya Kira Kurdawa Su Fito Jefa Kuri'a

Shugaban yankin Kurdawan Iraki, Massoud Barzani, ya yi kira ga Kurdawa dasu fito zaben raba gardama da za'a kada kuri'arsa a gobe Litini.

Barzani ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai dazu a birnin Erbil, inda ya ce duk wani yunkuri na neman hulda da gwamnatin Bagadaza ya cutura.

Zaben raba gardama a cewarsa shi ne matakin farko kan yadda Kurdistan za ta bayyana mahangarta, sannan kuma a shiga aiwatar da shirin.

Barzani ya kara da cewa'' muna da yakinin cewa samun yancin kai shi ne zai hana maimaita mummunan abunda ya faru a baya, don haka muna son tattaunawa da gwamnatin Bagadaza don shawo kan sabanin, aman hakan zai dau shekara guda ko biyu.

Dama kafin hakan Barzani ya ce amuncewa da shirin ba wai yana nufin ballewa nan take ne ba, face dai bude wani sabon babi na tattaunawar gaske da gwamnatin Bagadaza.

Gwamnatin Iraki dai ta bakin firayi ministan ta Haider al-Abadi ta maida martani tana mai cewa za ta dauki duk matakan da suka dace domin kare martaba da hadin kan kasar, bayan kiran a fito zaben na raba gardama da shugaban yankin Kurdawan Massoud Barzani ya yi.