Iraki : Zaman Dar-dar Na Tilastawa Baki Ficewa Daga Kurdistan
(last modified Thu, 28 Sep 2017 15:16:51 GMT )
Sep 28, 2017 15:16 UTC
  • Filin jirgin sama na yankin Erbil
    Filin jirgin sama na yankin Erbil

Sakamakon zaman dar-dar da ake ciki a Kurdistan na Iraki bayan zaben raba gardama da aka gudanar 'yan kasashen waje na ficewa daga yankin.

Zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan nan da ya samu amuncewar Kurdawan na Iraki don ballewa daga Iraki, ya bar baya da kura inda jama'a da dama ke cikin zaman dar-dar.

Rahotanni daga yankin sun ce baki daga kasashen ketare na tururuwa zuwa filayen jiragen sama domin barin yankin, sakamakon wa'addin zuwa gobe juma'a da gwamnatin Bagadaza ta bayar na dakatar da zirga- zirga jiragen sama na kasa da kasa zuwa Erbil a matsayin maida martani ga hukumomin na Kurdistan kan zaben raba garadama da aka gudanar.

Da yewa daga cikin bakin sun ce kasashen su ne ko kamfanonin da sukewa aiki suka bukace su fice daga yankin saboda halin rashin tabas da aka shiga.

Shi ma karamin ofishin jakadancin faransa a yankin ya bukaci 'yan kasarsa da basu da takardar visa ta Iraki dasu fice yankin kafin gobe Juma'a.