Sojojin Yamen Sun Kashe Sojojin Hayar Masarautar Saudiyya Masu Yawa
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankunan kudancin Saudiyya, inda suka kashe sojojin hayar Saudiyya masu yawa.
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sansanin rundunar sojin kawancen Saudiyya na Al-Dal'ah da ke garin Najran a kudancin kasar Saudiyya, inda suka kashe sojojin haya masu yawa tare da jikkata wasu adadi na daban. Kamar yadda sojojin na Yamen suka yi luguden makamai masu linzami kan tawagar sojojin hayar Saudiyya a babbar hanyar Khidrah da ke garin na Najran.
Har ila yau sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kai farmaki kan sansanin sojojin hayar Saudiyya da ke Jabali-Ashqari, inda suka kashe sojojin hayar Saudiyya masu yawa tare da kwasar ganimar makamai.
A gefe guda kuma jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan yankuna daban daban da suke lardin Sa'adah na kasar Yamen tare da janyo hasarar rayuka da na dukiyoyi.
Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ne mahukuntan Saudiyya suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen da sunan dawo da tsohon shugabann kasar mai ritaya Abdu-Rabbuh Mansur Hadi kan karagar mulkin kasar lamarin da a halin yanzu ya janyo hasarar dubban rayukan al'ummar Yamen tare da tilastawa wasu miliyoyi yin gudun hijira daga muhallinsu.