Firayi Ministan Iraki Na Ziyara A Turkiyya
(last modified Wed, 25 Oct 2017 11:19:52 GMT )
Oct 25, 2017 11:19 UTC
  • Firayi Ministan Iraki Na Ziyara A Turkiyya

Firayi ministan Iraki, Haidar al-Abadi, ya gana da shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erodgan a wata ziyara da ya soma yau a birnin Ankara.

A wannan ziyara kuma Mista Abadi zai gana da takwaransa, Binali Yildirim inda zasu tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Babban abunda bangarorin zasu tattauna bai wuce batun zaben raba gardama na Kurdistan ta Iraki ba da kasashen biyu ke adawa da shi ba.

Ziyara dai ta zo ne a daidai lokacin da Kurdawan Iraki suka yi gwamnatin Bagadaza tayin jingine sakamakon zaben raba gardaman da aka gudanar yau da wata guda cif.