Ana Gab Da Kawo Karshen 'Yan Ta'addar Da'esh A Siriya
Bayan kwashe shekaru uku karkashin mamayar 'yan ta'addar IS, magajin garin Deir Ezzor, Ali Karami ya sanar da komawar garin karkashin milkin gwamnatin siriya.
A ranar juma'ar da ta gabata, ma'aikatar tsaron kasar Siriya ta tabbatar da tsarkake garin Deir Ezzor, baki dayansa daga mamayar 'yan ta'addar IS tare da tabbatar da doka da oda da cikinsa, sannan ta ce dakarun tsaron kasar za su ci gaba da yaki har sai sun tabbatar da tsarkake kasar baki daya daga 'yan ta'adda.
A halin yanzu garin Boukmal dake kan iyakar kasar da Iraki ne kadai ya rage a hanun 'yan ta'addar IS a jihar Deir Ezzor, ganin mahimancin wannan jihar an iya bayyana cewa nasarar da dakarun tsaron siriya da kawayensu suka samu a jihar Deir Ezzor na a matsayin gab da kawo karshen 'yan ta'addar da'esh a cikin kasar, na biyu, idan aka la'akari da halin da kungiyar IS take ciki a kasar Iraki kusa da kan iyakar Siriya a garin Ka'im, hallaka ko meka yuwa shi kadai ne ya ragewa mayakan kungiyar IS a kasashen biyu, tsarkake jihar Deir Ezzor na a matsayin yanke duk wata alaka ta kai kawo da kai dauki a tsakanin mayakan 'yan ta'addar IS a tsakanin kasashen siriya da Iraki, kuma na a matsayin tabbatar da tsaron a kan iyakokin kasashen.
Wannan nasara ta dakarun Siriya,akalla nada muhimmnaci guda biyu, na farko mahimanci tabbatar da tsaro a garin Deir Ezzor saboda matsayin da yake da shi na hada yankunan gabashi zuwa yankunan arewaci da kuma tsakiyar kasar, kuma shi ne hanyar dake hada yankunan Badiyatu-Sham da Aljazera, da kuma kasar Iraki, kari a kan hakan, ganin cewa Deir Ezzor gari na kiwo da noma yana matsayi mai mahimanci game tattalin arzikin kasar kuma ya nada arzikin karkshin kasa da suka hada da isakar gaz gami da man fetir.
Jaridar alyaumu-sabi'i wacce ake bugawa a birnin Londan, jiya juma'a ta wallafa makalar Abdulbari Atwan shugaban jaridar kuma masanin harakokin siyasar gabas ta tsakiya inda ya rubuta cewa (Bayan da ikon kasar Siriya sama da kashi 95% ya koma karkashin Dakarun tsaron siriya da kuma kawar da hadarin kungiyar IS, da kuma killace mayakan kungiyar 'yan ta'addar jabhatu-nusra a garin Idlib dake arewa maso gabashin kasar, ana iya cewa wasan siyasa ya canza tsakanin masu bayan gwamnatin siriya da masu goyon bayan 'yan ta'adda.
Tushen masu yaki da ta'addanci a siriya, wato kasashen Iran, Rasha, Siriya da kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi sun canza yanayin da ake ciki a faden daga bisa amfanin sojojin Siriya, a bagare guda kuma kawancen Amuka masu goyon bayan 'yan ta'adda sun kwashi kashinsu a hannu.
Wannan nasara da dakarun siriya tare kawayensu ke samu kan 'yan ta'adda a kasar na zuwa ne, yayin da a ranar larabar da ta gabata gwamnatin haramcecciyar kasar Isra'ila ta sake kai hari ta sama a wasu yankunan kasar siriya, wannan kuma na zuwa ne cikin jarin hare-haren da ta saba kaiwa cikin kasar, wannan hari na a matsayin irin fishi da bakin cikin da magoya bayan 'yan ta'addar suka shiga sanadiyar nasarar da sojojin siriyar ke samu a kan 'yan ta'adda.
Duk da irin kokarin da Amurka tare kawayenta suke yi na ganin kungiyar ta'addancin IS ta ci gaba da rike wasu yankuna a kasashen siriya da iraki, to amma 'yanto garin Deir Ezzor na a matsayin gab da kawo karshen kungiyar IS a Siriya.