Sojojin Iraki Sun Kwace Ikon Kauyuka Da Dama Daga IS
A ci gaba da farmakin da suke kan 'yan ta'adda na kungiyar IS ko Da'esh, sojojin Iraki sun yi nasara kauce ikon kauwuka da dama da suka dade karkashin kungiyar a yankin hamada dake yammacin kasar a iyaka da Siriya.
Sojojin hadin gwiwa da dakarun sa kai sun kwace birnin Roummana da gadarsa da kuma wasu kauyuka goma kamar yadda babban kwamandan rundinar, Janar Abdelamir Yarallah, ya sanar cikin wata sanarwa.
kauyan Roummana na a yankin al-Qaïm tsakiyar sansanin karshe na 'yan ta'addan IS wanda sojojin Iraki suka kauto a ranar uku ga watan nan.
Wannan dai na zuwa ne bayan kaddamar da farmakin kwato Rawa yanki na karshe da har yanzu yake karkashin ikon yan ta'addan.
A halin da ake ciki dai sojojin na Iraki na ci gaba da dannawa a kokarin tsakake ilahirin yankin dake a hamadar yammacin kasar a cewar firayi ministan kasar Haider al-Abadi.