Sojojin Kasar Yamen Sun Kame Sojojin Hayar Masarautar Saudiyya Masu Yawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i2563-sojojin_kasar_yamen_sun_kame_sojojin_hayar_masarautar_saudiyya_masu_yawa
Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi sun yi nasarar kashe tarin sojojin hayar masarautar Saudiyya masu yawa tare da jikkata wasu adadi baya ga kame gungun sojojin hayar fiye da 170 a lardin Baidha.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 17, 2016 02:16 UTC
  • Sojojin Kasar Yamen Sun Kame Sojojin Hayar Masarautar Saudiyya Masu Yawa

Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi sun yi nasarar kashe tarin sojojin hayar masarautar Saudiyya masu yawa tare da jikkata wasu adadi baya ga kame gungun sojojin hayar fiye da 170 a lardin Baidha.

Gidan talabijin din Al-Masirah a yammcin jiya Laraba ya nuna hoton bidiyo na sojojin hayar masarautar Saudiyya 176 da suka fito daga kasashen Larabawa daban daban da sojojin gwamnatin Yamen gami da dakarun sa-kai na mabiya Huthi suka kame a garin Al-Wadiyyah da ke lardin Al-Baidha.

Rahoton gidan talabijin na Al-Masirah ya bayyana cewa; Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa-kan sun yi ruwan makamai masu linzami ne kan tawagar sojojin hayar masarautar ta Saudiyya ne a kan hanyarsu ta komawa sansaninsu da ke lardin Ma'arib, inda suka kashe da dama daga cikinsu, don haka sojojin hayar da suka tsira da rayuwarsu tsakanin wadanda suka jikkata da masu lafiya suka mika kansu a matsayin fursunonin yaki.