Rahoton Hukumar UNICEF Kan Halin Da Yara Suke A Kasar Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25739-rahoton_hukumar_unicef_kan_halin_da_yara_suke_a_kasar_yemen
Asusun kula da yara na MDD UNICEF a takaice ya bada rahoton cewa yara dubu 23 daga shekara ta 2016 ya zuwa yanzu suka rasa rayukansu a kasar Yemen sanadiyyar hare-haren kasar Saudia da kawayenta a kan kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:02+00:00 )
Nov 25, 2017 06:21 UTC
  • Rahoton Hukumar UNICEF Kan Halin Da Yara Suke A Kasar Yemen

Asusun kula da yara na MDD UNICEF a takaice ya bada rahoton cewa yara dubu 23 daga shekara ta 2016 ya zuwa yanzu suka rasa rayukansu a kasar Yemen sanadiyyar hare-haren kasar Saudia da kawayenta a kan kasar.

Kamfanin dillancin labaran Anatolia na kasar Turkia ya nakalto hukumar kula da yara ta MDD tana fadar haka a jiya jumma'a ta kuma kara da cewa a shekara ta 2016 da ta gabata iyaye mara dubu 4, 272 aka kashe a yayinda jarirai dubu 23 suka mutu sanadiyarra yakin da gwamnatin kasar saudia take jagoranta a kan mutanen kasar Yemen. 

Banda haka rahoton ya kara da cewa, akwai yara kimani dubu 400 a halin yanzu suna fama da tsananin karancin ainci mai gina jiki, kuma idan ba'a kawo masu daukin gaggawa ba suna iyaka mutuwa. 

A cikin rahotanninta na baya, majalisar dinkin duniya ta dorawa gwamnatin kasar saudia da kawayenta laifin mummunan halin da mutanen Yemen suke ciki na barzana mutuwa sanadiyarra rashin aminci. 

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudia tare da tallafawar Amurka da kasashen yamma, take jagorantar yakin kwace iko a kasar Yemen domin maida wani dan korenta wanda ya rasa shugabancin kasar , wato Abdu Rabbu hadi mansur kan kujerar shugabancin kasar.