Birtaniya Ta Bukaci Saudiyya Ta Kawo Karshen Killace Kasar Yemen
Jaridar Daily Telegram ta ambato ministan raya kasashe na Birtaniya Penny Mvrdant tana cewa; Babu wani dalili da Saudiyyar take da shi na hana shigar da kayan agaji zuwa cikin kasar ta Yemen.
Ministar ta gargadi Saudiyyar da cewa idan har ta ci gaba da keta dokokin kasa da kasa, to alakar da ke tsakaninta da Birntaniya za ta sami koma baya.
Har ila yau Penny Mvrdant ta ce; A halin da ake ciki da akwai kananan yara 400,000 da ke cikin kasar ta Yemen da suke da matsalar abinci maras gina jiki, kuma matukar ba a shigar da kayan abinci cikin kasar ta Yemen ba, to adadin wadanda za su mutu zai karu.
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suna yin kira ga Saudiyyar da ta sauya siyasarta akan kasar Yemen bayan da ta jefa al'ummar kasar cikin bala'oin kwalara da kuma yunwa.
Fiye da shekaru biyu kenan Saudiyyar tana yaki da al'ummar Yemen ba tare da ta cimma abinda ta yi nufi ba.