Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula 11
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26587-yemen_jiragen_yakin_saudiyya_sun_kashe_fararen_hula_11
A jiya alhamis ne dai jiragen yakin Saudiyyar suka kai hare-hare a babban birnin kasar San'aa da kuma yankin Sa'adah da ke arewacin kasar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Dec 22, 2017 03:04 UTC
  • Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula 11

A jiya alhamis ne dai jiragen yakin Saudiyyar suka kai hare-hare a babban birnin kasar San'aa da kuma yankin Sa'adah da ke arewacin kasar.

Baya ga mutane 11 da suka rasa rayukansu, wasu 8 kuma sun jikkata.

Tun a 2015 ne dai Saudiyyar bisa cikakken goyon bayan Amurka, ta fara kai wa kasar Yemen harin soja wanda har yanzu yake ci gaba. Hare-haren na Saudiyya sun kashe mutane fiye da 13,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.

A gefe daya killacewar da Kasar Saudiyyar ta yi wa Yemen ta haddasa bullar yunwa da kuma cutar kwalara wacce kawo ya zuwa yanzu mutane miliyan 1 suka kamu da ita.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Rights Watch"  ta bukaci da a shigar da sunan yarima muhammad Bin Salman  na Saudiyya cikin jerin sunayen masu aikata manyan laifukan yaki domin hukunta shi Yemen.