Sojojin Yamen Sun Kakkabo Jirgin Saman Yakin Rundunar Kawancen Saudiyya
Sojojin Yamen da dakarun kungiyar Ansarullah na kasar sun kakkabo wani jirgin saman yakin rundunar kawancen masarautar Saudiyya da ke kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yamen.
Tashar talabijin na Al-Masiriyyah na kasar Yamen ya watsa rahoton cewa: Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullah sun yi nasarar kakkabo jirgin saman yakin rundunar kawancen Saudiyya da ke kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar a yau Lahadi.
Rahoton ya kara da cewa: An kakkabo jirgin yakin ne nau'in Tornado kirar kasar Birtaniya a lardin Sa'adah da ke shiyar arewacin kasar Yamen.
A gefe guda kuma majiyar sojin Yamen ta sanar da cewa: A shekarar da ta gabata ta 2017, sojojin kasar sun samu nasarar kakkabo jiragen saman yakin rundunar kawancen Saudiyya 29 tare da tarwatsa motoci da tankokin yaki 1,569.