Gwamnatin Yemen Ta Bukaci Tattaunawa Kai Tsaye Da Gwamnatin Kasar Saudiya
Priministan kasar Yemen ya bukaci tattaunawa kai tsaye da gwamnatin kasar Saudiya wacce take yakar mutanen kasar ta Yemen ba tare da tattaunawar ta hada da tsohon shugaban kasar Abdu rabbu hadi Mansur ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Abdulaziz bin Habtur Priministan kasra ta Yemen yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacin da yake ganawa da mataimakin jakadan majalisar dinkin duniya ta musamman a kasar ta Yemen Mu'in Shuraim a birnin Sana'a.
Abdul Aziz ya kara da cewa a halin yanzu tsohon shugaban kasar bai da ta cewa dangane da abin da ya shafi sulhuntawa tsakanin bangarorin biyu. Sai kuma batun wahalhalun da mutane kasar Yemen suke ciki Priministan ya fadawar jami'am majalisar dinkin duniya kan ce wa kashi 1/3 na mutanen kasar suna cikin mummunan hali na rashina abinci da magunguna, don haka ya bukaci Majalisar dinkin duniya ta yi kokarin ganin an kawo karshen killacewar da ake yi wa kasar don kayayyakin agaji su sami shiga don tallafawa wadannan mabukata.
A nashi bangaren Mu'in Shuraim mataimakin jakadan Majalisar dinkin duniya a Yemen ya bayya cewa kokarin da Majalisar take yi shi ne tabbatar da an samar da zaman lafiya a kasar tare da yardar dukkan bangarorin biyu.