Yemen: Sojoji Sun Kashe 'Yan Koren Saudiyya Masu Yawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27375-yemen_sojoji_sun_kashe_'yan_koren_saudiyya_masu_yawa
Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen ta ce; An kashe 'yan koren Saudiyyar 20 ne a wani hari da sojoji suka kai a yankin Al-Jawf da ke arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:18+00:00 )
Jan 18, 2018 04:18 UTC
  • Yemen:  Sojoji Sun Kashe 'Yan Koren Saudiyya Masu Yawa

Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen ta ce; An kashe 'yan koren Saudiyyar 20 ne a wani hari da sojoji suka kai a yankin Al-Jawf da ke arewacin kasar

Bugu da yankin Ma'arib da ke tsakiyar kasar ta Yemen, wani kwararren maharbi na sojan Yemen ya kashe 'yan koren na Saudiyya 16.

Saudiyya dai ta shelanta yaki ne akan kasa da al'ummar Yemen tun a 2015 wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka. A bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya adadin wadanda suka rasa rayukansu sun kai 13,000.

Kasar ta Yemen ta fama da karancin abinci da kuma magani a asibitoci saboda killace ta da kasar Saduiyya ta yi.

Dubban mutane ne suke mutuwa saboda yunwa da kuma kamuwa da cutar kwalara.