Wata Kotun Iraki Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan 'Yar Jamus
Jan 21, 2018 10:51 UTC
Wata kotu a birnin Bagadaza na Iraki ta yankewa wata 'yar asalin kasar Jamus hukuncin kisa, saboda alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.
Kotun mai kula da harkokin da suka shafi ta'addanci a Iraki, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan matar wacce ba'a bayyana sunan ta ba.
An dai tuhumi matar ne da taimakawa kungiyar 'yan ta'addan da kayan aiki domin kai hare-hare a kasashen Siriya da Iraki, kamar yadda wata sanarwa da kakakin kotun, mai shari'a Abdel Settar Bayraqdar ya fitar a yau Lahadi.
Tags