Afganistan : Taliban Ta Dau Alhakin Kai Harin Otel Intercontinental
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27477-afganistan_taliban_ta_dau_alhakin_kai_harin_otel_intercontinental
Kungiyar Taliban ta sanar da cewa ita ke da alhakin kai harin nan da ya yi ajalin mutum a kalla 6 a Otel din Intercontinental dake Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.
(last modified 2018-08-22T11:31:18+00:00 )
Jan 21, 2018 10:54 UTC
  • Afganistan : Taliban Ta Dau Alhakin Kai Harin Otel Intercontinental

Kungiyar Taliban ta sanar da cewa ita ke da alhakin kai harin nan da ya yi ajalin mutum a kalla 6 a Otel din Intercontinental dake Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

Wata sanarwa da kakakin kungiyar, Zabiullah Mujahid, ya aike ta (email) ta ce mayakanta Taliban din biyar ne suka kaddamar da harin. 

Kafin hakan dai ma'aikatar cikin gidan kasar ta Afganistan ta fitar da sanarwar cewa an kawo karshen harin tare da kashe duk maharan da kuma kubutar da mutanen dake cikin ginin su 146 ciki har da baki 41.  

A cikin daren jiya Asabar ne, mayakan suka kai hari a otel din bayan an kammala wani babban taron fasahohin sadarwa.