'Yan A Ware A Yemen Sun Kwace Fadar Gwamnatin Aden
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27719-'yan_a_ware_a_yemen_sun_kwace_fadar_gwamnatin_aden
Rahotanni daga Yemen na cewa mayakan 'yan Kudu masu neman ballewa daga kasar sun kwace iko da fadar gwamnatin Aden birnin na biyu mafi girma a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:21+00:00 )
Jan 28, 2018 13:15 UTC
  • 'Yan A Ware A Yemen Sun Kwace Fadar Gwamnatin Aden

Rahotanni daga Yemen na cewa mayakan 'yan Kudu masu neman ballewa daga kasar sun kwace iko da fadar gwamnatin Aden birnin na biyu mafi girma a kasar.

Hakan ya biyo bayan kazamin fadan da suka gwabza da dakarun gwamnati mai murabus a birnin na Aden.

Bayanai daga kasar sun ce an samu hasara rayukan mutane a kalla 15 ciki har da fararen hula 3 da kuma wasu kimanin 30 da suka jikkata. 

A halin da ake cikin shugaban kasar mai murabus dake gudun hijira a Saudiyya, Abd Rabbo Mansour Hadi, ya bukaci dakarun dake masa biyaya dasu tsagaita bude wuta ba tare da wata wata ba.

Yau Lahadi ne dai wa'adin da masu fafatukar a ware na kudancin kasar suka baida gwamnatin mai murabus na ta aiwatar da wasu sauye sauye a cikin gwamnatin ya kare, saidai kasancewar gwamnatin bata aiwatar da hakan ba, mayakan suka nemi shiga birnin na Aden lamarin da ya rikide zuwa rikici tsakaninsu da dakarun gwamnatin.