Yemen : Rayuka Na Ci Gaba Da Salwanta A Aden
Rahotanni daga Yemen na cewa ana ci gaba da gwabza fada a birnin Aden tsakanin mayakan masu fafatukar a ware da kuma dakarun gwamnatin mai murabus.
Wasu alkalumma da kungiyar agaji ta Red Cross ta fitar sun nuna cewa mutane 36 ne suka rasa rayukansu kana wasu 185 suka raunana a cikin kwanaki nan.
Tun da farko dai wasu bayanai sun ce mutane 24 ne suka rasa rayukansu da suka hada da fararen hula da kuma mayaka.
Ana dai gwabza fadan ne da manyan makamai ciki har da tankunan yaki.
A ranar Lahadi data gabata ne fada ya barke tsakanin dakarun dake biyaya ga shugaban kasar mai murabus Abd Rabbo Mansour Hadi da samun goyon bayan Saudiyya, da kuma mayakan 'yan kudu masu neman ballewa da ke samun goyon bayan Hadaddiyar Daular Larabawa UAE.
Halin da ake ciki a wannan kasa ta Yemen dai ya kara dagula al'amurra a kasar dake fama da yaki da Saudiyya ke jagoranta kan kasar yau kusan shekaru uku.