Ma'aikatar Tsaron Isra'ila Ta Kira Taron Gaggawa.
Ministan Tsaron Isra'ila ya kira taron gaggawa tare da halartar Gadi Eizenkot babban hafsan sojojin Isra'ila da wasu manyan janar janar domin tattauna yanayin da suke ciki da siriya.
Wannan taro na zuwa ne bayan da Dakarun tsaron sararin samaniyar siriya suka kakkabo jirgin yakin Haramtacciyar kasar Isra'ila samfarin F-16 a tudan Golan.jim kadan bayan kakkabo wannan jirgi, wasu jiragen yakin Isra'ilan sun kai hare-hare a gefen Damuscus na kasar ta Siriya.
Bisa rahoton da tashar HKI ta 10 ta biyar, a karshen wannan taro, an bawa dakarun saman Isra'ila damar ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Siriya.
To sai dai wasu kafafen yada Labaran Isra'ilan sun sanar da rufe filin jirgin Ben Gurion dake arewacin HKI da kuma sararin samaniyar Isra'ila daga arewaci zuwa birnin Tel-Aviv na wani lokaci, sannan kuma an buga karaurawar hadari ga mazauna yankin Golan da Jalil Ulya, inda mazauna yankin suka buya.