Ziyarar Sa'ad Hariri Zuwa Saudiya
(last modified Wed, 28 Feb 2018 06:19:23 GMT )
Feb 28, 2018 06:19 UTC
  • Ziyarar Sa'ad Hariri Zuwa Saudiya

Piraministan kasar Labnon ya amsa goron gayyatar hukumomin saudiya a wannan Laraba, inda da jijjifin safiyar yau ya tashi daga birnin Bairout zuwa birnin Riyad

Kafafen yada labaran kasar Labnon sun habarta cewa a safiyar yau laraba, Piraministan kasar Labnon Sa'ad Hariri zai ziyarci kasar Saudiya, inda zai gana da sarki Salman bn Abdul-aziz da yarima mai jiran gado Muhamad bn salman a birnin Riyad.

Wannan ziyara ta Piraministan kasar Labnon na zuwa ne bayan ziyararsa ta karshe a watan Nuwambar shekarar 2017 din da ta gabata, wacce a cikinta ne ya sanar da murabus din sa daga kasar ta Saudiya,

Da dama daga cikin masana na ganin cewa murabus din Hariri a wancan lokaci na zuwa ne bisa matsin lamba na hukumomin saudiya, har ma shugaban kasar ta Labnon Micheal Aun ya sanar da cewa mahukuntan saudiya sun kama Piraministan kasarsa a birnin Riyad.

Bayan shiga tsakanin kasar Faransa , sa'ad Hariri ya koma kasar sa tare da janye murabin din nasa inda ya ciki gaba da aikinsa a matsayin sa na Piraministan kasar Labnon.