Afganistan : Taliban Ta Yi Watsi Da Tayin Gwamnati Na Tattaunawa
(last modified Thu, 01 Mar 2018 11:16:49 GMT )
Mar 01, 2018 11:16 UTC
  • Afganistan : Taliban Ta Yi Watsi Da Tayin Gwamnati Na Tattaunawa

Kungiyar Taliban a Afganistan ta yi fatali da tayin gwamnatin kasar na bude tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu.

Wannan dai ya zo ne bayan da shugaban kasar Afganistan, Ashraf Ghani, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta manta komi, don kuma dauke haramcin tafiye-tafiye ga 'yan Taliban wadanda suka rungumi shirin zaman lafiya, amma da sharadin su amunce da kundin tsarin mulkin kasar, da martaba 'yancin 'yan kasa musamman mata da kuma jami'an tsaro.

Kafin hakan dai kungiyar ta Taliban ta aike wa Amurka da sakon neman tattaunar zaman lafiya, a yayin da tayi watsi da tayin gwamnatin Afganistan na tattaunar zaman lafiya.

A jiya ne dai aka kammala wani taron kasa da kasa na lalubo hanyoyin samar da zaman lafiya a kasar ta Afganistan wanda ya samu halartar tawagogi daga kasashen duniya 25.