Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare
Harin bayan na da Saudiyyar ta kai a cikin birnin Sanaa ya ci ran mutum da kuma jikkata wasu da dama
Tashar talabijin din al-Masirah ta bada labarin cewa; Jiragenn yakin Saudiyyar sun kai hari a yankuna al-jabalul Aswad da Bani Madhar da suke a babban birnin kasar Sanaa.
Bugu da kari jiragen yakin Saudiyyar sun kai wasu hare-haren a yankin al-mahit da ke gundumar Sa'aadh a arewacin kasar.
A gefe daya, wani kwararren maharbin sojan Yeman ya halaka sojan Saudiyya daya a yankin JIzan da ke kudancin kasar. Bugu da kari sojojin Yemen sun kai hari akan sojojin Saudiyya a kauyen Kamar da ke gundumar ta Jizan a cikin kasar Saudiyya.
Tun a 2015 ne dai sojojin Saudiyya suka shelanta yaki akan kasar Yeman wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.