Yemen: Sojojin Saudiyya Hudu Sun Halaka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29001-yemen_sojojin_saudiyya_hudu_sun_halaka
Tashar talabijin din al-masirah ta kasar Yemen ta bada labarin cewa wani kwararren maharbin soja ne ya halaka sojojin na Saudiyya a gundumar jizan da ke kudancin Saudiyya.
(last modified 2018-08-22T07:01:33+00:00 )
Mar 12, 2018 05:52 UTC
  • Yemen: Sojojin Saudiyya Hudu Sun Halaka

Tashar talabijin din al-masirah ta kasar Yemen ta bada labarin cewa wani kwararren maharbin soja ne ya halaka sojojin na Saudiyya a gundumar jizan da ke kudancin Saudiyya.

A wani gefen sojojin kasar Yemen sun harba manyan bindigogi akan sansanin sojojin Saudiyya da 'yan korensu a kudu maso gabacin gundumar Jizan. Sai dai babu cikakken rahoto akan asarar da harin ya haddasa.

Saudiyya ta fara jagorantar kai wa kasar Yemen hari tun a 2015, sannan kuma ta killace kasar ta sama da kasa da kuma ruwa.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa a cikin shekaru uku na yakin, mutane fiye da 13,000 ne Saudiyyar ta kashe.