Yemen: An kashe Sojojin Kasar Saudiyya Biyar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29187-yemen_an_kashe_sojojin_kasar_saudiyya_biyar
Sojojin Yemen Sun kashe sojojin saudiyya biyar a yankin Jizan da ke kudancin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:34+00:00 )
Mar 18, 2018 08:41 UTC
  •  Yemen: An kashe Sojojin Kasar Saudiyya Biyar

Sojojin Yemen Sun kashe sojojin saudiyya biyar a yankin Jizan da ke kudancin kasar

Kamfanin dillancin labarun Sputnik na kasar Rasha ya ce an kashe sojojin ne a kauyen Kawiyyi da ke gundumar Jizan.Bugu da kari sojojin kasar ta Yemen sun harba manyan bindigogi akan sansanin sojan Saudiyya da yake a al-Haskul inda da dama daga cikin sojojin su ka halaka.

A cikin saharar Medi, sojojin Yemen da kuma dakarun sa-kai na Ansarullah sun halaka 'yan koren Saudiyyar da dama.

Shekaru uku kenan ajere da Saudiyya take yaki da al'ummar Yemen, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 13,000.