An Hallaka Jalal Baleedi, Jagoran Kungiyar Da'esh A Yemen
-
Jalal Baleedi, Jagoran Kungiyar (IS) A Yemen
Jalal Baleedi,ya dai hallaka ne tare da wasu 'yan ta'ada 12 a wani harin jiragai marasa matuki a birnin Rawda.
Rahotanni daga kasar Yemen na cewa jagoran 'yan ta'adan Da'esh a kasar Yemen Jalal Baleedi ya hallaka a wasu hare-haren jiragen sama maras matuki a birnin Rawda dake lardin Shabwa.
Masu aiko da rahotanni sun ce harin da aka kai kan wata mota a lardin Abyan ya kashe duk mutane shida dake cikin motar ciki harda Jalal Baleedi din wanda ke zamen kuma jagoran kungiyar Al'Qaida a kasar ta Yemen.
Baleedi dai na da hannu a hare-haren ta'adanci da dama a kasar ta Yemen.
Wasu majiyoyi a kasar sun ce da asubahin yau ne wasu jiragen yakin Amurka suka kai hari kan motar da Baleedi din yake ciki inda suka hallaka shi tare da wasu mukaraban sa uku akan hanyar Chaqrah-zanzibar.