Shugaban Siriya Ya Ziyarci Sojojin Kasar Da Suke Yankin Ghouta
(last modified Sun, 18 Mar 2018 16:15:07 GMT )
Mar 18, 2018 16:15 UTC
  • Shugaban Siriya Ya Ziyarci Sojojin Kasar Da Suke Yankin Ghouta

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ya kai ziyara sansanonin sojojin kasar da suke kai yankin Gabashin Ghouta da ke wajen birnin Damaskus, babban birnin kasar, inda ya tattauna da sojojin da jin yanyin da suke ciki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Siriyan (SANA) ya bayyana cewar a yau ne shugaba Asad din ya kai ziyarar ce don gane wa idanuwansa halin da ake ciki da kuma irin nasarorin da dakarun nasa suka samu a kan 'yan ta'addan da suke rike da yankin na tsawon lokaci.

Kafar watsa labaran na SANA ya watsa hotunan ziyarar inda shugaba Asad din ya zaga bangarori daban-daban na yankin da kuma tattaunawa da sojoji da nufin kara karfafa musu gwuiwan fadan da suke yi da 'yan ta'addan da kuma fatattakarsu daga yankin.

A kwanakin baya ne dai sojojin Siriya bisa taimakon kawayensu suka kaddadamar da hare-hare na nufin kwato yankin na Ghouta da kuma tseratar da fararen hula da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da  su bugu da kari kan tsarkake yankin daga 'yan ta'addan wadanda a lokuta da dama suke amfani da wajen wajen kai hare-hare zuwa birnin Damaskus, babban birnin kasar Siriya.