An Kashe Fararen Hula 6 A Iraki
Mar 21, 2018 06:32 UTC
Kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta kai hari kan wurin binciken jami'an tsaro tare da kashe mutane 6
Hukumar gidan radio da talabijin ta kasar Iran ta nakalto kwamandan kungiyar sa kai ta kasar Iraki ( Hashadu-Sha'abi) na cewa 'yan ta'addar ISIS sun kai hari kan wurin bincike na jami'an tsaron kasar dake tsakanin yankin Turkhormatu da Dakuk dake da nisan kilomita 130 dake yammacin Bagdaza babban birnin kasar, inda suka kashe mutane 6 tare da jikkata wasu 21 na daban.
Duk da cewa, an karya lagon 'yan ta'adda a kasar ta Iraki, amma har yanzu akwai wasu daga cikin su da suka buya a yankuna daban daban na cikin kasar,inda suke ci gaba da kaddamar da hare-haren ta'addancin kan fararen hula.
Tags