Afganistan : Harin Ta'addanci Ya Kashe Mutum 26 A Kabul
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane a kalla 26 ne galibi samari suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa a Kabul babban birnin kasar.
An dai kai harin ne a harabar jami'ar Kabul, a daidai lokacin da mutanen ke bukin murnar shiga sabuwar shekara hijira shamsiyya wacce aka fi sani da Nowrooz.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu mutane 18 da suka raunana, a cewar mukadashin kakakin ma'aikatar cikin gidan kasar, Nasrat Rahimi.
Al'kalumman da ma'aikatar kiwan lafiya ta kasar ta fitar sune mutum 31 ne suka rasu, kana wasu 65 suka raunana kuma adadin wadanda suka mutu mai yiwa ya karu saboda masu munanen raunuka da dama da aka samu.
Wannan harin shi ne irinsa na biyar da ake kai a babban birnin kasar a kasa da mako guda.