Apr 05, 2018 06:34 UTC
  • Syria: An Gano Wani Kurkuku Da 'Yan Ta'adda Ke Tsare Mutane A Ghuta Ta Gabas

Sojojin kasar Syria sun sanar da gano kurkukun ne a garin Zamalka da ke yankin Ghuta wanda kuma kungiyar 'yan ta'addar "Failaq-Rahman' take tafiyar da shi.

Kamfanin dillancin labarun kasar Syria "Sana' ya ambato minitsan cikin gida Muhammad Sha'ar yana cewa; A halin da ake ciki yanzu, tuni 'yan sanda sun koma aiki ka'in da na'in domin tabbatar da tsaro a yankin na Ghuta ta gabas.

Sojojin kasar ta Syria sun kuma sanar da  tashin gobara a cikin rumbun manyan makamai na kungiyar 'yan ta'adda ta "Tahrir Sham' a garin al-Nairab da gefen garin Adlib. Babu cikakken bayani akan abin da ya haddasa gobarar.

Sojojin Syria tare da kawayenta sun sami nasarar fatattakar 'yan ta'adda daga yankin na Ghuta ta gabas.

Tags