Assad: Babban Makamin Makiya Musulmi Shi Ne Rarraba Kan Al'umma
Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya bayyana cewa; yada rarraba tsakanin al'umma da kuma yada tsattsauran ra'ayi da sunan addini, su ne manyan makaman da makiya suke yin amfani da su a halin yanzu domin raunana al'ummar musulmi a duniya.
Shugaba Assad ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin tawagar masu mahalarta taron hadin kan al'umma da aka gudanar a birnin Damascus na Syria, inda ya ce makiya al'ummar musulmi tare da hadin baki da wasu daga cikin musulmin da suka sayar da imaninsu da lamirinsu domin neman samun kusanci da makiya, suna yin aike tare dare da rana, domin rusa al'ummar musulmi, tare da bata sunan addinin muslunci a idon duniya, ta yadda suke mayar ma'anan musulunci ta koma ta'addanci a wajen sauran al'ummomi wadanda ba musulmi ba.
Shugaba Assad ya ce nauyi ne da ya rataya kan malamai daga cikin musulmi, da su wayar da kan musulmin musamman wadanda ake yaudara saboda jahilcinsu kan addini, kamar yadda kuma nauyi na malamai su fadakar da duniya kan hakikanin abin da ake kira addinin muslunci, addinin zaman lafiya da kyawawan dabi'u da fahimtar juna da kuma girmama dan adam.
A jiya ne aka kammala zaman taron hadin kan al'ummar musulmi a birnin Damscus, wanda ya samu halaratr malamai daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da Masar, Morocco, Tunisia, Aljeriya, Indonesia, Turkiya, India, Lebanon, Iraki, Afghanistan da sauransu.