Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kai Farmaki Kan Palastinawa
Jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan matasan Palastinawan da suka taru a sansanin Auda dake gabashin Khan Yunus
Cibiyar sadarwar Palastinu ta habarta tun da safiyar yau juma'a al'ummar Palastinu suka fito domin neman 'yancinsu da na dawo da yankunansu da aka mamaye, inda suka taru a dandali-dandali a kuma manyan hanyoyin yankunan kauyen Khazana, dake gbashin yankin zirin Gaza, sun fuskanki farmaki daga jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila.
Yanzu yanzu dai ba a bayyana hasarar rayuka ko dukiyar da wannan hari ya janyo.
Matasan Palastinawan na da niyar kona tutar haramtacciyar kasar Isra'ila a lunguna daban-daban a kan iyaka da zirin Gaza, wannan dai ita juma'a ta uku a jere da Al'ummar Palastinu ke gudanar da zanga-zangar neman a dawo da hakokkinsu da aka mamaye.