Al'ummar Kasar Labnon Sun Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa.
(last modified Sun, 06 May 2018 19:07:23 GMT )
May 06, 2018 19:07 UTC
  • Al'ummar Kasar Labnon Sun Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa.

Shugaban Majalisar dokokin kasar Labnon ya bayyana zaben a matsayin zaben jin ra'ayin al'umma kan ci gaba da gwagwarmaya, kiyaye hadin kan al'ummar kasa, da kuma tsarkake kasar daga mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila.

A wannan lahadi ce, al'ummar kasar Labnon suka gudanar da zaben 'yan majalisa a karon farko cikin tsawon shekaru tara, da misalin karfe 7 na kasar Labnon aka buda runfunar zaben, inda manyan jami'an gwamnatin kasar suka fara kada kuri'unsu, sannan da misalin karfe 7 na yammacin yau ne aka rufe runfunan zaben, inda tuni aka fara kidaya kuru'un

A yayin da ya kada kuri'ansa, Shugaban kasar ta Labnon Michel Aun yace  majalisar Kasar ita ce tushen cibiyar siyasar kasar sannan ya tabbatar da cewa wannan rana daga cikin mahiman ranaiku na siyasa da kuma fayyace zabin al'ummar kasar Labnon.

A nasa Bangare Piraministan kasar Sa'ad Hariri yayin da ya kada kuri'arsa ya ce Yau ranar salla ce ga tafarkin demokaradiya na al'ummar kasar Labnon, kuma halartar da na yi na wannan zabe, na sauke nauyin da ya rataya kaina na dan kasar.

Ministan cikin gidan kasar Nehad Manshuk ya yaba da irin matakan tsaron da aka dauka a yayin gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin.

Kafin gudanar da zaben na yau, an dage shi har so uku saboda wasu matsaloli na tsaro da na siyasa, lamarin da ya sanya aka yi ta sabinta wa'adin 'yan majalisar.