Jiragen Yakin Kawancen Sun Kashe Dukkanin Iyalin Wani Gida A Yemen
Harin wuce gona da irin da kawancen Saudiya ke ci gaba da kaiwa kasar yemen yayin sanadiyar shahadar mutane biyar 'yan gida guda a jihar Sa'ada dake arewacin kasar
Tashar Talabijin din Almasira ta kasar Yemen ta habarta cewa a marecen jiya Laraba jiragen yakin kawancen Saudiya sun yi lugudar wuta a garin Dahiyan na jihar Sa'ada, inda suka rugurguza wani gida, da ya yi sanadiyar shahadar wata mata tare da 'yayanta 4.
Har ila yau Bam din da sojojin hayar Saudiya suka jefa wani gida dake kauyen Razih yayi sanadiyar wani karamin yaro tare da jikkatar ma'aifinsa da ma'aifiyarsa.
A cikin 'yan kwanakin nan kauyukan Azzahir, Shada Da Razih dake kan iyalan kasar da Saudiya na fuskantar hare-haren makamai masu Linzami da na Sojojin hayar sanudiya.
Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.
A halin da ake ciki , kasar ta Yemen na fama da cutar kwalara wacce hare-haren na Saudiyya suka jawo ta ta hanyar gurbata ruwan sha.