Yemen: Saudiyya Ta Sake Amfani Da Bama-baman Da Aka Haramta
Tashar talabijin al-masdar News ta Yemen ta ba da labarin cewa; A ranar juma'ar da ta gabata Saudiyyar ta yi amfani da makamai masu kwafso a yankin Hamadan da ke babban birnin kasar Sanaa
Rahoton ya ci gaba da cewa; Kawo ya zuwa yanzu mutane shida ne su ka rasa rayukansu, biyu daga cikinsu kananan yara.
Bugu da kari rahoton ya ci gaba da cewa; Amurka tana bai wa Saudiyyar dukkanin taimako na hotunan tauraron dan'adam da dabarun yaki akan al'ummar kasar ta Yemen.
Tare da cewa an haramta amfani bama-bamai masu kwafso, amma kasashen Amurka, Birtaniya suna sayar wa Saudiyya, wanda kuma take amfani da su.
Saudiyyar ta shelanta yaki akan kasar Yemen tun a 2015 bisa cikakken goyon bayan Amurka da Birtaniya