'Yan Sahayoniya Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus
(last modified Thu, 17 May 2018 18:57:34 GMT )
May 17, 2018 18:57 UTC
  • 'Yan Sahayoniya Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus

A yau alhamis da musulmin palasdinu su ka fara azumin watan Ramadhan, 'gwamman 'yan sahayoniya sun kutsa cikin masallacin kudus

Kamfanin dillancin labarun Palasdinawa na "Ma'a" ya ce;Yahudawa 'yan share wuri zauna wadanda jami'an tsaro suke yi wa rakiya sun shiga cikin farfajiyar masallacin na Kudus, daga kofar Babul-Magaribah"

Bugu da kari 'yan sahayoniyar sun rika farfasa abubuwa masu amfani a cikin masallacin adidai lokacin da dubban palasdinawa suke salla.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da 'yan share wuri zauna suke kutsawa cikin masallacin Kudus da zummar tsokanar musulmi.

A cikin wannan makon ne dai Amurka ta mai da ofishin jakadancinta cikin birnin na Kudus, duk da cewa da akwai kudurorin majalisar Dinkin Duniya da suke magana akan rashin gaban kai, akan birnin har sai bayan cimma yarjejeniya da palasdinawa