Shugaban Rundunar Sojin Amurka Ya Gargadi Gwamnatin Kasar Siriya
(last modified Fri, 01 Jun 2018 13:46:05 GMT )
Jun 01, 2018 13:46 UTC
  • Shugaban Rundunar Sojin Amurka Ya Gargadi Gwamnatin Kasar Siriya

Shugaban rundunar sojin kasar Amurka ya gargadi gwamnatin Bashar Asad ta Siriya kan ta nisanci yin amfani da karfi a kan yankunan Kurdawar kasarta da suke shiyar arewa maso gabashin kasar ta Siriya.

A jawabin da ya fitar a cikin daren jiya Alhamis: Shugaban rundunar sojin Amurka Kenneth MacKenzie ya bayyana cewar dukkanin kungiyoyin da suke cikin kasar Siriya su sani cewa kaddamar da harin soji kan sojojin Amurka ko kawayenta a kasar ta Siriya zata fuskanci mai da martani mai gauni.

Gamayyar kungiyoyin Kurdawa masu dauke da makamai ta "Syrian Democratic Forces" da take yankunan arewa maso gabashin kasar Siriya tana samun goyon bayan kasar Amurka musamman mallaka mata makamai.

Wannan gargadi ta shugaban rundunar sojin Amurka ya zo ne bayan furucin da shugaban kasar Siriya Bashar Asad ya yi a wata hira da tashar Russian Today ta kasar Rasha da a cikin ya bayyana cewa: Idan tattaunawa da gamayyar kungiyoyin Kurdawa ta cutura, to babu makawa gwamnatin Siriya zata yi amfani da karfi wajen kwato yankunan arewa maso gabashin kasar daga mamayar mayakan Kurdawan.