Mutanen Aljeriya Sun Bukaci Ficewar Kasar Daga Kungiyar Kasashen Larabawa
Wani zaben jin ra'ayin da aka gabatar a kasar Algeria ya nuna cewa mafi yawan mutanen kasar suna son kasar ta fice daga kungiyar kasashen Larabawa.
Shafin yanar gizo na jaridar "Alkhabar" ta kasar Algeria ta rubuta a shafinta na yanar gizo kan cewa sakamakon wani zaben jin ra'ayin da ta gudanar ya nuna cewa kashe 82 % na mutanen Algeria basa ganin kimar kungiyar kasashen Larabawa, kuma suna bukatar ficewa daga kungiyar.
A cikin makon da ya gabata ma shugaban kungiyar yan kwadago na kasar ta Algeria Luwizeh Hanun , a jawabin da ya gabatar bayan wata zanga zangar nuna goyon bayan Palasdinawa ya bayyana cewa kungiyar kasashen Larabwa da HKI kamar dan juma ne da dan jummai babu bambanci a tsakaninin.Hanun ya kara da cewa kungiyar kasashen larabawa ta zama wurin taro ne na shuwagabannin kasar Larabawa, amma bata da wani tasiri a ko ina a duniya.