Mutanen Aljeriya Sun Bukaci Ficewar Kasar Daga Kungiyar Kasashen Larabawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31386-mutanen_aljeriya_sun_bukaci_ficewar_kasar_daga_kungiyar_kasashen_larabawa
Wani zaben jin ra'ayin da aka gabatar a kasar Algeria ya nuna cewa mafi yawan mutanen kasar suna son kasar ta fice daga kungiyar kasashen Larabawa.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 03, 2018 12:05 UTC
  • Mutanen Aljeriya Sun Bukaci Ficewar Kasar Daga Kungiyar Kasashen Larabawa

Wani zaben jin ra'ayin da aka gabatar a kasar Algeria ya nuna cewa mafi yawan mutanen kasar suna son kasar ta fice daga kungiyar kasashen Larabawa.

Shafin yanar gizo na jaridar "Alkhabar" ta kasar Algeria ta rubuta a shafinta na yanar gizo kan cewa sakamakon wani zaben jin ra'ayin da ta gudanar ya nuna cewa kashe 82 % na mutanen Algeria basa ganin kimar kungiyar kasashen Larabawa, kuma suna bukatar ficewa daga kungiyar.

A cikin makon da ya gabata ma shugaban kungiyar yan kwadago na kasar ta Algeria Luwizeh Hanun , a jawabin da ya gabatar bayan wata zanga zangar nuna goyon bayan Palasdinawa ya bayyana cewa kungiyar kasashen Larabwa da HKI kamar dan juma ne da dan jummai babu bambanci a tsakaninin.Hanun ya kara da cewa kungiyar kasashen larabawa ta zama wurin taro ne na shuwagabannin kasar Larabawa, amma bata da wani tasiri a ko ina a duniya.