Afganistan: Taliban Ta Amince Da Tsagaita Wuta Don Karshen Ramadan
Kungiyar 'yan ta'adda ta taliban ta sanar da tsagaita buda wuta tsakaninta da sojojin Afganistan, a karshen watan Ramadan, wanda kuma shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 17 bayan da sojojin kasashen ketare karkashin jagorancin Amurka suka kawar da mulkin daga hannun 'yan taliban din.
Shirin tsagaita wutar dai zai fara daga ranar 27 ga watan Ramadana, har zuwa kwana biyar na karamar Sallah ko Aid-el-Fitr", wato daga ranar 12 zuwa 19 ga watan Yuni nan, kamar yadda kungiyar ta sanar a manhajarta ta WhatsApp, saidai kungiyar ta ce zata iya dakatar da shirin da zarar an farma mata.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan sanarwar da shugaban kasar ta Afganistan, Ashraf Ghani, ya bayar na tsagaita wuta.
Saidai sa'o'i kadan kafin sanarwar, 'yan ta'addan na Taliban sun kai hare hare a wata barikin soji dake lardin Herat a yammacin kasar a Jiya Juma'a, da kuma wani harin a wani ofishin 'yan sanda dake lardin Kunduz a arewacin da jijibin safiyar wannan ranar ta Asabar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaron kasar ta Afganistan 36.
A kwanan nan dai wani gungun manyan malamai a kasar ta Afganistan, ya fitar da wata ''Fatawa'' inda ya bayyana ta'addanci a matsayin abunda ya sabawa koyar wa ta addinin Islama.