Afganistan : Taliban Ta Yi Watsi Da Kiran Tsawaita Tsagaita Wuta
(last modified Sun, 17 Jun 2018 16:54:32 GMT )
Jun 17, 2018 16:54 UTC
  • Afganistan : Taliban Ta Yi Watsi Da Kiran Tsawaita Tsagaita Wuta

Kungiyar Taliban a Afganistan ta yi watsi da kiran shugaban kasar, Ashraf Ghani, na tsawaita tsagaita wuta a dalilin karshen watan Ramadan.

Tunda farko dai an yi tsammanin shirin zai taimaka sosai wajen samar da zaman lafiya a wannan kasa da rikicin gomman shekaru ya daidaita.

Jim kadan dai bayan sanawar da taliban, an kai wani harin kunar bakin wake a wani lardi dake gabashin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 18 da kuma raunana wasu kimanin hamsin.

Da yammacin yau Lahadi ne shirin tsagaita wutar da aka cimma a karshen watan Ramadan ke kawo karshe, saidai kakakin kungiyar ta taliban, Zabihullah Mujahid, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, basu da wata anniyar ta tsawaita tsagaita wuta, zasu ci gaba da ayyukansu da yardar Allah, tare da yin barazanar shiga yaki tun daga ranar Litini.

A jiya Asabar ne shugaban kasar ta Afganistan, ya sanar da shirin gwamnatin kasar na tsawaita tsagaita wuta, tare da kira ga kungiyar ta taliban da ita ma tayi koyi da hakan.

Matakin gwamntin kasar ta Afganistan dai ya samu yabo daga kungiyoyi da kasashen duniya da dama.