Kawancen Saudiya Ya Hallaka Mutun 8 A Arewacin Yemen
Jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari jahar Sa'ada na arewacin kasar, inda suka kashe fararen hula da dama.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto tashar talbijin Almasira ta kasar yemen na cewa a ci gaba da ta'addancin kawacen Saudiya a kasar a yau Talata jiragen yakin kawancen saudiya sun yi ruwan bama-bamai kan wasu gungun mutane dake bikin aure a kauyen Zahira na jahar Sa'ada dake arewacin kasar, inda suka kashe akalla mutane takwas tare da jikkata wasu 6 na daban.
A jiya Litinin ma wani Jirgin saman yakin masarautar Saudiyya ya yi luguden wuta kan wata makarantan yara da wani gidan cin abinci a kauyukan Zubaid da Attahayta da suke lardin Hudaudah , lamarin da ya janyo hasarar rayukan daliban makaranta uku tare da jikkata wasu uku na daban.
Jiragen yakin saudiya na kai hare-haren ta'addancin a wuraren biki ko na ta'aziya sakamakon taruwar jama'a mai yawa a wurin, inda ko a ranar 23 ga watan Avrilun da ya gabata, jiragen yakin kawancen Saudiyar suka kai hari wajen bikin aure a kauyen Raakat dake yankin Bani Kais na jahar Hajah dake arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 33 tare da jikkata wasu 55 na daban.