A Cikin Watanni 6 Isra'ila Ta Kame Falastinawa 3,533
Rahotanni daga Palestine sun tabbatar da cewa a cikin watanni 6 da suka gabata ya zuwa yanzu Isra'ila ta kame Falastinawa 3533.
Shafin yada labarai na Amun ya bayar da ke cewa, bisa kididdigar da cibiyar kula da fusrsunonin Falastinawa da ke kurkukun Isra'ila gami da cibiyar kare hakkin bil adama ta Falastinu suka bayar, daga farkon shekarar nan ta 2018 Isra'ila ta kame Falastinawa 3533.
Rahoton ya ce 651 daga cikin wadanda aka kananan yara ne, 63 kuma daga cikinsu 'yan mata ne, haka nan kuma akwai 'yan jarida guda 4 da suke tsare.
Dukkanin wadannan Falastinawa dai Isra'ila tana tsare da su ne a birane daban-daban, da hakan ya hada da Quds, Ramallah, Janin, Khalil, Bait lahm, Nablus, Tuklkaram, Kalkiliyya, Tubas, Gaza da sauransu.
Ya zuwa yanzu akwai Falastinawa 6000 da suke garkamer a gidajen kason Isra'ila ba tare da sanin makomarsu ba.