MDD: Wajibi Ne A Kawo Karshen Killace Yankin Gaza
Jul 16, 2018 06:50 UTC
Babban Jami'in Mai kula da ayyukan MDD a yankin Gabas ta tsakiya ne ya bayyana bukatar a kawo karshe killacewar da aka yi wa yankin na Gaza
Bayan da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta sami nasara a zabukan da aka yi a 2006 ne haramtacciyar Kasar Isra'ila ta killace yankin na Gaza tare da hana kai da komowar muhimman kayan masarufi a cikinsa.
Nickolay Mladenov ya ce; Gaza tana cikin mummunan yanayi, kuma al'ummarta na fuskantar matsaloli masu yawa.
Jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma nuna goyon bayansa akan Zanga-zangar da mutanen Gaza suke yi na kiran da a dauke musu takunkumi, sannan ya yi kira ga haramtacciyar kasar Isra'ila da ta daina kai wa kananan yara hari.
Tags