IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Afganistan
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS, ta ce ita keda alhakin kai harin kunar bakin wake da aka kaddamar a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan a jiya Lahadi.
'Yan sanda a kasar sun ce mutane 11 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 14 kuma suka jikkata a harin.
Harin kunar bakin waken dai ya auku ne da yammaci jiya, kan titin zuwa filin jirgin saman kasa da kasa na Kabul, a daidai lokacin da tawagar mataimakin shugaban kasar ta Janar Abdul Rashid Dostum da ya koma kasar ke wucewa.
Galibin wadanda lamarin ya rusa da su fararen hula ne wandanda suka halarci wurin don tarbar Janar Dostum din, sai kuma wani jami'in 'yan sanda guda daya.
Majiyoyin asibiti, sun ce mutane 48 ne suka samu raunuka, kuma tuni aka garzaya da su asibitoci don ba su kulawa.