"Yan Gudun Hijira Na Kasar Syria sun Fara koma wa Gida
(last modified Tue, 24 Jul 2018 12:45:59 GMT )
Jul 24, 2018 12:45 UTC

Shugaban cibiyar tafiyar da tsarin mulki a ma'aikatar tsaron kasar Rasha Mikhail Mezentsev ne ya snaar da cewa an bude manyan wurare shiga da fice domin ba da dama ga yan gudun hijirar Syria da su koma gida

Jami'in na kasar Rasha ya kara da cewa; An bude kan iyakoki da kasashen Jordan da Lebanon saboda ba da dama ga 'yan gudun hijira da su koma gidajensu, kuma tuni an kafa cibiyoyi a cikin kasar Syria domin maraba da su.

Rahoton ya ci gaba da cewa kawo ya zuwa yanzu mutane 850 ne suka fara tafiyar komawa gida.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha   Nikolay Bortsov ya sanar da cewa; Ana ci gaba da yin kokari domin ganin an daukewa kasar Suriya takunkumin da aka kakaba mata, saboda a sami damar taimaka wa 'yan gudun hijira.