Palasdinu: "Yan Sandan Sahayoniya Sun Kai Wa Masallacin Kudus Hari
A jiya juma'a ne 'yan sandan sahayoniya su ka kai wa masu salla a masallacin kudus hari ta hanyar harba abubuwa masu kara
Kamfanin dillancin labarun Fars ta ambato majiyar Palasdinawa na cewa; Baya ga amfani da bama-bamai masu sauti, sun kuma harba hayaki mai sa hawaye akan masu sallar, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar da dama daga cikinsu.
Majiyar palasdinawan ta ci gaba da cewa; An kuma yi taho mu gama a tsakanin 'yan sandan da kuma sojojin sahayoniya a gefe daya, da kuma Paladinawa a daya gefen a kusa babul magaribah da ke masallacin mai alfarma.
Kai wa masallacin kudus hari ya zama abin da sojoji da 'yan sanda da kuma yahudawa 'yan share wuri zauna suke yi kusan kowane mako.
"Yan sahayoniyar na son rushe masallacin kudus ne da gina wajen bautarsu a bagirensa.