Harin Ta'addancin Ya Kashe Mutane A Garin Halab Na Siriya
Kungiyar 'yan ta'adda ta kai hari garin Halab dake arewacin kasar Siriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutum 9.
A marecen jiya alhamis, 'yan ta'adda a siriya sun kai hari da makamin iguwa a garin halab na arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 4 tare kuma da jikkata wasu biyar na daban.
Majiyar garin ta ce 'yan ta'addar sun kai harin ne da nufin rusa dandalin tsakiyar birnin dake dauke da cibiyar samar da ruwan sha na garin.
Kwanaki biyu da suka gabata 'yan ta'addar sun kai hari yankin Hamdaniya na garin Halab din, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula biyu da kuma jikkatar wasu bakwai na daban.
Wannan hari na zuwa ne a yayin da gwamnatin Siriya ke shirye-shiryen dawo da 'yan gudun hijra zuwa gidajensu, kuma tuni gwamnatin ta Halab ta fara sabunta gidajen da suka da rusa a yankin.