Dakarun Yemen Sun Kakkabo Jirgin Leken Asiri Na Kawancen Saudiya
Majiyar kasar Yemen ta sanar da kakkabo wani jirgi maras matuki na leken asirin kawancen saudiya a jahar Aljawf dake arewacin kasar
Tashar Talabijin din Almasira ta kasar Yemen ta sanar da cewa a wannan lahadi dakarun tsaron sararin samaniyar kasar sun samu nasarar kakkabo wani jirgi maras matuki na leken asirin kawancen saudiya a lardin Maslub na jahar Aljawf dake arewacin kasar.
Wannan dai shi ne jirgi maras matuki na kawancen saudiyar na biyu da aka kakkabo a lardin na maslub cikin wannan wata na Augusta da muke ciki.kafin hakan dai, a watan Mayun da ya gabata dakarun tsaron kasar ta yemen da na sa kai sun kakkabo jirage maras matuka uku na kawancen saudiyar a yankunan Asir, Jaazan dake kudancin saudiya.
Duk da irin killacewar da dakarun kawancen saudiyar suka yi wa kasar Yemen, amma a ko wata rana karfin kariya na dakarun tsaron kasar ta yemen da dakarun sa kai na kara karuwa.
Tun watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya da hadaddiyar daular larabawa bisa taimako da kuma goyon Amurka suka fara kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen, tare da killace kasar ta kasa, sama da kuma ta ruwa, wannan lamari dai ya yi salwanta rayukan yamaniyawa sama da dubu 14, gami da jikkata wasu dubai na daban da kuma raba wasu milyoyi da mahalinsu.