Sep 04, 2018 18:12 UTC
  • Hamas: Gwagwarmaya Ce Kadai Hanyar Kalubalantar Laifukan 'Yan Sahayoniya

A wani bayani da kungiyar ta gwagwarmaya ta fitar ta ce; Har yanzu haramtacciyar kasar Isra'ila tana ci gaba da tafka laifuka a yankin yammacin kogin Jordan.

Bayanin ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga al'ummar Palasdinu da su yi aiki da dukkanin abin da suke da shi wajen kalubalantar 'yan mamaya, domin babu harshe da 'yan sahayoniya suke fahimta idan ba karfi ba.

Hamas ta ci gaba da cewa; "Yan sahayoniya suna ci gaba da kai hare-hare na zalunci da kama palasdinawa haka nan kuma rusa gidajen mutane, wanda manufarsa shi ne sake mamaye yankuna.

Hamas ta kuma bayyana cewa; Al'ummar Palasdinu ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare hakkokinsu, kuma a karshe za su yi nasarar korar 'yan mamaya.

Tags