Kungiyar Huthi Ta Zargi Saudia Da Alhakin Hana Tawagarta Zuwa Geneva
(last modified Sat, 08 Sep 2018 06:46:57 GMT )
Sep 08, 2018 06:46 UTC
  • Kungiyar Huthi Ta Zargi Saudia Da Alhakin Hana Tawagarta Zuwa Geneva

Dubban daruruwan mutanen kasar Yemen sun gudanar da zanga zangar yin allawadai da kawancen kasar Saudia wanda ya hana tawagar kasar zuwa birnin Geneva don halattan taron sulhun da MDD ta shirya a kasar Swizland.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Yemen tana cewa tawagarta a shirye take ta halarci taron, amma MDD ta ki cika bukatun da suka mika mata na, da farko gwamnatin kasar Omman ta bada jirgin sama wanda zai kaisu Genevan tare da wasu wadanda basa da lafiya a kasar, sannan ta lamunce masu kan cewa zasu dawo gida.  Friday, Loay al-Shamy jami'in gwamnatin kasar ta Yemen ya kara da cewa ba zasu amince a bincike jirgin da zasu yi tafiya da shi a Njibuti ba kamar yadda kawancen Saudia suke so ba.,

Gwamnatin kasar Saudia da kawayenta wadanda suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa , Morocco da Sudan sun fadawa kasar Yemen da yaki a ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015 da nufin maida dan korensu Abdu rabbu Hadi Mansur kan kujerar shugabancin kasar. 

Kungiyar ta Huthi ce take kula da al-amuran gwamnatin kasar tun bayan fara yakin wanda ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane kimani dubu 15. Sannan wasu miliyoyi suna fama da yunwa ko kuma suna gudun nhijira a ciki da wajen kasar.